Tuesday 3 October 2017

TAUHIDI (kadaita Allah)

TAUHIDI (kadaita Allah)


Dasunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai
TAUHIDI (kad'aita Allah)
Shine kadaita Allah a cikin Bauta shi kadai batare da hadashi da wani ba, kuma shine Addinin da aka aiko Annabawa dashi gaba dayaAllah yakara masu Aminci, kuma Allah baze karbi wani Addini ba inba shiba, kuma baya karban Ayyukan bayi se dashi, domin shine Asalin da ake gina Addini akanshi, kuma duk sanda aka rasashi to aikin bawa baze amfane shiba. KARKASUWAN TAUHIDI Tauhidi yakasu zuwa kashi uku (3):
1. Tauhidin Rububiyyah (Reno) Shine kudurce cewa Allah, shine wanda ya halicci, dukkan halittu, yake azurtasu, kuma wannan Nau’i na Tauhidi babu wanda yake musunshi, har mushrikan farko sun tabbatar dashi, kamar su Abu Jahal, fir’auma ne kawai wanda yatabayin musun babu ubangiji, sun kasance suna shedawa cewa Allah shine wanda yake halitta, yake gudanar dakomai dake cikin duniya, shike rayawa, yake kashewa, Allah madaukakin Sarki yace “Kuma idan kuka tambayesu wanene wanda yahalicci Sammai da Kassai, yake gudanar da Rana da Wata? Tabbas zasuce maka shine Allah…..( Sur.Ankabut: 61) Se ikirarin dasu kayi be shigar dasu musulunci ba, kuma baze tseratar dasu daga Azaba ba, kuma bata kare masu dukiyoyinsu da dukiyoyinsu ba, saboda basu tabbatar da Tauhidin Uluhiyyah, sun hada Allah da wani cikin bauta.
2. Tauhidin Uluuhiyyah (Bauta) Shine kadaita Allah acikin dukkan Ayyukan bauta da ake kusanci zuwa ga Allah dasu, kamar Addu’a da Tsoro,da Fata, da Dogaro, da Kwadayi, da Tsorata, da Neman temako, da neman biyan bukaya, da yin yanka da Alwashi da makamantansu. Kuma Allah yasaukarwa manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam (“Kace an umarceni ne da in bautawa Allah ina me kadaita masa Addini” Sur. Zumar 11.) wato bauta Saboda haka mutum baze juya wani daga cikin ibada bag a wani daya daga cikin mala’iku ko wani Annabi ko wani Waliyyi ko Shehi, domin hakki ne na Allah, wanda kon yaba wanda bashi ba to yayi Shirka.
3. Tauhidin Asmaa’u was Siffat Shine imani da cewa Allah yana da zati wanda baya kama da sauran zatuttuka, yana da siffofin da b asa kamada sauran siffofi, kuma sunayensa suna nuni ne nuni na yanke shakka akan abinda abinda yake dashi na siffofin cika wayo kamala kai tsaye. Allah Subhanahu Wata’ala yace (“Babu wani abu da yayi kama dashi kuma shi me jine me gani “ Sur. Shuurah 11.) kuma da tabbatar da abinda Allah ya tabbatar ma kansa acikin littafinsa (Al’qur’ani)ko manzansa yatabbatar masa dashi tabbatarwa wacce take dacewa da girma da daukakarsa ba tare da kamantashi da wani abu ba, ko kwatantashi da wani ba, ko kore masa sifar, ko lankwasa ma’anarsa, ko yanda yake, baza muyi kokarin kamanta wani sashi na cikin siffofinsa ba da zukatanmu ko da tunaninmu, A’ah zmu bar abin kamar yanda yabamu labari. TO YAYA ZAMU SAMU TAUHIDI?
Zamu iya zama masu tauhidi ne, ta hanyar sanin Allah, wanene shi? da sanin hakikaninsa, a ilmance da kuma aiki da hakan, kuma shine Rai tajawu ko zuciya zuwa gareshi da soyaiya, da tsoro, da komawa zuwa gareshi, da dogaro akanshi, da Addu’a, da tsarkakeshi, da girmamashi da kuma yimasa bauta. Atakaice dai kada yazamana a zuciyar dan Adam daba na Allah ba, kuma bawa yazama baya nufin Allah da Shirka ko Bid’ah ko Sabo karaminsa da babbansa,kuma kada ya nuina kiyaiya ga duk abinda Allah yayi Umarni dashi to wannan tauhidi da kansa wato Laa ilaa ha illal Lah. MENENE MA’ANAR LAA’ILAA’HA ILLAL LAHU?
Ma’ana shine babu abin da’ake bautawa da cancanta a Sama da Kasa face Allah shi kadai baya da abokin taraiya, domin abubuwan da’ake bauta mawa baatattu suna da yawa, se dai abinda ya can-can ci bautan shine Allah shi kadai.Allah Subhanahu Wata’ala yace: (“ Saboda haka Allah shine Ubangiji na gaskiya, kuma tabbas an\binda suke kira wanda bashi baataccene, kuma lallai Allah shine madaukaki kuma me girma” Sur.alhajj:62) ba ma’anarta ba Babu mahalicci se Allah kamar yadda wadansu jahilai suke tsammani, domin kafiran Kuraishawa wanda Allah ya’aikoda manzo a cikinsu sun kasance suna sheda cewa Allah shine mahalicci me gudanar da al’amuran duniya shi kadai baya da abokin taraiya kamar yanda Allah yace: (“Shin yanzu za’a sanya Abin bauta yazama ubangiji guda daya Lallai wannan abune me ban mamaki” Sur. Saad:5) sun fahimci cewa wannan kalma lallai tana bata bautawa duk wanda ba Allah ba, kuma tana takaita bauta ga Allah shi kadai sukuma basa son haka, saboda hakane manzan Allah ya yakesu har se sun Shaida da Laa ilaa ha illal laahu kum subata hakkinta, shine kadaita Allah da bauta shi kadai. Wanna ke bata ikirarin da wadansu keyi cewa ma’anar Laa ila ha illal laahu shine kace Allah yana nan kuma shine wanda yayi halitta, yake gudanar da al’amura kuma wanda yayi hakan yana da Tauhidi koda yayi ma wani bauta kamar Rokon wadanda suka mutu suke cikin kabari,d yimusu alwashi, da neman kusancinAllah tahanyarsu, da neman Albarka (tabarruki) da yin dawafi a kabarbura da neman albarka da kasar kabarin kamar yanda muke ganin a kabarin Shehu dan fodio dake sokoto. Hakika kafiran Kuraishawa sun san cewa Laa ilaa ha illal lahu tana bukatan aiki shine barin bautawa wanda ba Allah ba, kuma idan suka fadeta suka cigaba da bauta ma gumaka to zasu war-ware musuluncinsu sukuma bas son haka sukeba, abin mamaki yau zaka musulmi suna bauta ma Allah kuma suna neman temakon wanda ba Allah, suna kiran sunayen wasu matattu na mutanen kwarai, suna war-ware musuluncinsu. Tur da wanda Abu jahal, da Abu lahab suka fisu sanin ma’anar laa ilaa ha illal lahu.
RUKUNNAN KALMAR TAUHIDI
Kalmar tauhidi tana da rukunnai guda biyu (2). korewa: tana kore bautan kowani irin abin bauta. Tabbatarwa: tana tabbatar da bauta ga Allah madaukakin Sarki shi kadai batareda hadashi da wani ba. MENENE KE WAR-WARE KALMAR TAUHIDI?
Abubuwan dasuke war-ware (bata) Kalmar tauhidi suna da yawa, amma ga wadansu daga ciki:
Na Farko: Shirka da Allah a cikin bauta , Allah madaukakin Sarki yace: (“Lallai Allah baya gafartama wanda yahada shi dawani, amma yana gafarta ma abinda ba haka ba (shirka) ga wanda yaso” Sur.Nisaa’i:116) kuma yace: (“lalai ne duk wanda yayi Shirka da Allah, to hakika Allah ya haramta masa Aljanna, kuma makomansa itace wuta, kuma Azzalumai basu da wani me temako” Sur.ma’idah:72) kuma yana daga cikin shirka, kiran wani da ba Allah ba, Idan wata musiba (fitina) tazo, yi ma Aljanu yanka ko kabari.
Na Biyu: Duk wanda yasanya wani tsakaninsa da Allah, yana Rokonsu, yana kiransu, yana neman cetonsu, yana dogaro a kansu, ya kafirta da ijmaa’in malaman musulunci.
Na Uku: Duk wanda be kafirta mushrikai ba ko yayi shakkan kafircinsu, ko yake gyara abinda suke akai kaman yan gurguzu. To ya kafirta.
Na Hudu: Duk wanda yake kudurin cewa shiryawan da ba ta Annabi ba, shi yafi cika da dai-dai akan shiryarwar manzan Allah Sallal lahu alaihi wasallam, ko hukuncin wani yafi hukuncinsa, kamar wanda yake fifita tsarin turawa akan Shri’ar musulunci to ya kafirta.
Na Biyar: Duk wanda ya kyamaci wani daga cikin abinda manzan Allah yazo dashi to koda yayi aiki dashi ya kafirta Allah madaukakin Sarki yace (“Hakan saboda kafirai sun kyamaci abinda Allah ya saukar se yabata ayyukansu”Sur.muhammad:9) Na Shida: Duk wanda yayi izgili da wani abu dake cikin Addinin da manzon Allah yazo dashi, ladan dake ciki, ko azaban dake ciki ya kafirta Allah madaukakin Sarki yace (“kace masu shin yanzu da Allah, da Ayoyinsa, da manzansa kuke yiwa izgili? Kada kukawo uzuri hakika kunzama kafirai bayan kuna masu imani...Sur.tauba:65-66)
Na bakwai: Sihiri duk wanda ya aikatashi ko ya yardaq dashi,ya kafirta Allah madaukakin Sarki yace: (“ kuma basa karantar da kowa sihiri – aljanu – face .........................................................................................
Na takwas: duk wanda.............. zamu cigaba isha Allah

Contact us 08131240056

No comments:

Post a Comment

ARBAUNA HADITH SHEIK JAAFAR MAHMUD ADAM Ana kiranshi da suna Al-Arba'unan

ARBAUNA HADITH SHEIK JAAFAR MAHMUD ADAM Ana kiranshi da suna Al-Arba'unan nawawiyya saboda jinginashi ga malami Al-imamu yahaya bn sh...