Tuesday 3 October 2017

YANDA AKE WANKAN JANABA DAGA MARIGAYI SHEK JAFAR

YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA DAI SAURAN SU.Daga Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam Kano.Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai 'siffatul ijza' (ta wadatar), kuma wacce ake kira 'siffatu kamal' (ta kamala).Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne: Idan kazo zaka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka. Farkon abin da zaka fara yi shi ne:zaka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka debo ka wanke gaban ka، a dai-dai lokacin da zaka wanke gaban ka a lokacin zaka kulla niyya ta wankan janaba (Ko waninsa) wanda yake wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma'ana kayi tsarki kenan، to daga nan kuma sai kayialwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah zakayi sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan zaka kyale shi ba zaka yi shiba, to daga nan sai ka tsoma hannunka guda biyua cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya bude a lokacin da maniyyi yake kokarin fita daga jikinka ya koma yanda yake, don gashin dan Adam yakan bude musammam gashin sa na ka, idan ka zuba ruwa a haka na iya haifar maka da ciwon kai ko wani abu daban, bayan haka sai ka debi ruwa a cikintafin hannun ka daya sai ka zuba a kanka ka tabbatar ya game ko'ina a kanka, ka sake kanfata na biyu ka tabbatar ya game ko'ina a kanka, haka nauku ka tabbatar ya game ko'ina a kanka.To idan kayi wannan sai ka debi ruwa ka game dukkanin jikin ka da shi kana mai farawa da bangaren jikin ka na dama kafin na hagu, sannan nahagu ka tabbatar ruwa ya taba ko'ina. To idan kayi wannan ne ka kammala, abu na karshe shi ne sai kawanke kafar ka ta dama sannan kafarka ta hagu shine cikon alwalar da ka riga ka faro. Wannan ita ce siffa ta kamala a wankan janaba.In wankan janaba ne haka zakayi, in na haila ne haka za'ayi inma wanka ne na biki haka mace zata yi, idan wankan jumu'a ne ma haka za'ayi, wankan idi ma haka zaka yi, banbanci kawai shi ne NIYYA.Idan mutum zai yi siffa ta 'Al ijza' wadda ta wadatar ba sai kayi alawa acikin ta ba, kana zuwa kayi niyyaryin wanka din kawai sai ka dauki ruwan ka watsa a jikin ka ya game ko'ina, inma wani kududdufi ne ko rami ko swimming pool sai kayi tsalle ka fada aciki, dama ka kulla niyyar ka kafin ka shiga, daga ka fito abin da zakayi shi ne abubuwa guda biyu, kurkurar baki da kuma shaka ruwa a hanci da facewa.Shike nan, kuma ya halatta kayi sallah da wannan wankan, Hadisi cikin Sahihu Muslim ya nuna haka.Sai dai wanda ya yi wanka na farko ya fika kamala saboda ya bi dukkan sharuddan, ya fika cikar kamala, ya fika lada.Kasancewar ba'ayi alwala ba ciki, wannan ka'idace ta malamai cewa karamin kari (HADATHUL ASGAR)idan sun hadu da babban kari (HADATHUL AKBAR) to da ka kawar da babban kari, karamin ma ya tafi. Amma ba lallai bane idan ka kawar da karamin ace babban ma ya tafi.Bissalam

No comments:

Post a Comment

ARBAUNA HADITH SHEIK JAAFAR MAHMUD ADAM Ana kiranshi da suna Al-Arba'unan

ARBAUNA HADITH SHEIK JAAFAR MAHMUD ADAM Ana kiranshi da suna Al-Arba'unan nawawiyya saboda jinginashi ga malami Al-imamu yahaya bn sh...